logo

HAUSA

Manzon musamman na kasar Sin kan batun yankin gabas ta tsakiya ya ziyarci Saudiyya

2023-10-27 14:48:22 CMG HAUSA

Manzon musamman na gwamnatin Sin mai kula da harkokin yankin gabas ta tsakiya Zhai Jun ya ziyarci Saudiyya a jiya, inda ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Waleed Elkhereji, tare da yin musanyar ra’ayi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki tsakanin Palasdinu da Isra’ila.

Zhai Jun ya ce, ana fuskantar yanayi mai tsakani tsakanin Palasdinu da Isra’ila, kuma Sin na bakin ciki matuka da asarar rayukan fararen hula da ake samu. A cewarsa, dole ne a tsagaita bude wuta, a kuma kwantar da hankali a wurin, ta yadda za a samar da damammaki masu kyau ga warware wannan matsala a siyasance.

A nasa bangare, Waleed Elkhereji ya yabawa matsayi mai adalci da Sin ta dade tana dauka kan batun, yana mai fatan hada kai da Sin don ingiza wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin tun da wuri. (Amina Xu)