logo

HAUSA

Kamata ya yi gwamnatin Amurka ta yi la’akari da dalilan karbuwar gwamnan jihar California a kasar Sin

2023-10-27 10:34:25 CMG HAUSA

 

Gwamnan California na kasar Amurka Gavin Newsom, yana ziyarar aiki a nan kasar Sin, kuma Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shi a ranar Laraba 25 ga watan nan.

Jaridar Daily Post ta Birtaniya ta ba da labarin cewa, shugabannin Sin sun yi matukar maraba da ziyarar mista Newsom. Baya ga haka, wasu kafofin yada labarai na ketare sun ba da sharhi cewa, wannan ya alamta cewa, Sin na dora muhimmanci, da kuma sa ran hadin kai tsakanin larduna daban-daban na Sin da jihohin Amurka.

Tun daga watan Yuni na bana, Xi Jinping ya gana da wasu baki daga Amurka, kamar su Bill Gates, shugaban asusun Bill da Melinda Gates, da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Henry Alfred Kissinger. Kana ya amsa wasikun da abokai Amurkawa suka aika masa, don ingiza hadin kai tsakanin yankunan kasashen biyu a fannoni daban-daban.

Sau da yawa, Xi Jinping ya sha bayyana ra’ayinsa cewa, tushen huldar Sin da Amurka shi ne kyautata dangantakar al’umommin biyu, kuma makomar huldar kasashen biyu na dogaro kan matasa. A wannan karo kuma, Xi ya kara da cewa, hadin kan yankuna daban-daban na kasashen biyu na karawa huldar kasashen biyu kuzari.

Yawan GDPn kasashen biyu ya kai 1 bisa 3 na dukkan duniya, inda yawan mutane da GDPn ya shafa ya kai kashi 1 cikin 4. Ban da wannan kuma, yawan kudaden cinikayyar kasashen biyu ya kai kashi 1 cikin 5, irin wadannan ci gaban da bangarorin biyu ke samu na da ma’ana matuka, kuma dole ne a kiyaye su.

Jihar California ta yi watsi da bambancin ra’ayi a fannin siyasa, ta rungumi ra’ayin hadin kai da samun ci gaba tare, wanda hakan ya zamowa ’yan siyasar Amurka abun koyi, saboda irin wannan hadin kai ya amfani al’ummomin bangarorin biyu.  (Amina Xu)