logo

HAUSA

CMG ta gabatar da bikin baje kolin al’adun Sin na musamman a “palace of nations”

2023-10-27 14:27:03 CMG HAUSA

A jiya Alhamis ne kafar CMG da ofishin MDD dake Geneva, da tawagar dindindin ta wakilan Sin dake Geneva, suka yi hadin gwiwar gabatar da bikin baje kolin al’adun Sin na musamman, a fadar kasashen duniya ta “palace of nations”.

Shugaban CMG Shen Haixiong, da shugaban kwamitin raya al’adu na ofishin MDD dake Geneva Francesco Pisano, da kuma zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Swizerland Chen Xu, sun halarci bikin tare da ba da jawabai.

Wakiliyar musamman mai ba da shawara kan harkokin siyasa da huldar abokantaka, a ofishin babban jami’in MDD dake Geneva Lidiya Grigoreva, da dai sauran hukumomin kasa da kasa na MDD dake Geneva, da zaunannun wakilan kasashe fiye da 30 sun halarci bikin.

Cikin jawabin da ya gabatar, Shen Haixiong ya ce, al’adun Sin na bayyana mutuncin Sinawa, da kuma bayyana abubuwa mafi kyau a cikin al’adun bil Adama. Kaza lika kasar Sin na dukufa kan farfado da al’adun ta a sabon zamani. A matsayin kafa mafi girma dake watsa labarai a dukkanin fannoni na dandalolin daban-daban, Shen ya ce CMG na sauke nauyin dake wuyansa na shaida ci gaban al’adu, da ingiza mu’amalar al’adu, ban da wannan kuma, tana kokarin hada tunani da kimiyya da fasaha tare, ta yadda al’umommin kasa da kasa za su sada zumanta, da tutunbar juna, don zamanintar da al’ummar duniya cikin hadin kai.

Yayin bikin na musamman na wannan karo, mai taken “Mafarin al’adun Sin da ci gabansa”, an yi amfani da kimiyya da fasahar zamani, don jagorantar masu kallo, ta yadda za su fahimci al’adun Sin masu tsawon tarihin fiye da shekaru 5000, da ma yadda ake samun ci gaba bisa wannan tushe. (Amina Xu)