logo

HAUSA

An gudanar da bikin mika sabon ginin majalissar dokokin Zimbabwe

2023-10-27 16:23:38 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya jinjinawa kasar Sin bisa tallafin ta na gina sabon zauren majalissar dokokin kasar, aikin da a cewar shugaban kasar muhimmin abun tarihi ne ga Zimbabwe.

Shugaba Mnangagwa, ya yi tsokacin ne a jiya Alhamis, yayin bikin mika sabon ginin da gwamnatin Sin ta tallafa wajen gudanarwa. Shugaban ya yaba da ginin, wanda ya ce yana cikin gine-gine na zamani masu kayatarwa a Zimbabwe, kana ya godewa gwamnatin Sin, bisa tallafin ta a fannin goyon bayan samar da tarin ababen more rayuwa a Zimbabwe, da kwazon maginan kasar wajen ganin an cimma nasarar aiki. 

Daga nan sai shugaban na Zimbabwe ya sha alwashin karfafa hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar sa da Sin, tare da koyi daga nasarorin ci gaban kasar Sin. Kaza lika, ya alkawarta kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin zamanantar da noma, da masana’antu, da bunkasa kwarewa da ci gaban sana’o’i.  (Saminu Alhassan)