logo

HAUSA

Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-17 dauke da ‘yan sama jannati

2023-10-26 17:27:34 CMG Hausa

A yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-17, dauke da 'yan sama jannati 3 wadanda za su zauna a sararin samaniya har na tsawon kimanin watanni shida, a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.

An harba kumbon ne, ta hanyar amfani da rokar Long March-2F, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin.

'yan sama jannati 3 wato su Tang Hongbo, Tang Shengjie da Jiang Xinlin, su ne ‘yan sama jannati mafi karancin shekaru tun da aka fara aikin gina tashar sararin samaniya ta Tiangong ta kasar Sin.

Tang Hongbo, wanda aka haife shi a shekara ta 1975, shi ne kwamandan tawagar, kuma tsohon dan sama jannati. Tang Shengjie, wanda aka haifa a shekarar 1989, sabuwar fuska ce a wannan aiki, kuma shi ne matashin dan sama jannatin da ya shiga tashar sararin samaniyar kasar Sin. Jiang Xinlin, wanda aka haifa a shekarar 1988, shi ma sabon shiga ne a aikin binciken sararin samaniya.

Za su gudanar da wasu ayyuka a wajen tashar, ciki har da shigar da kaya masu nauyi da aikin kula da tashar sararin samaniya da sauransu.