logo

HAUSA

Rundunar sojin Sudan da dakarun RSF sun fara sabon zagayen tattaunawa a Saudiyya

2023-10-26 10:26:18 CMG Hausa

Rundunar sojin Sudan da dakarun RSF sun sanar da cewa, wakilansu sun isa birnin Jedda na Saudiyya a jiya, domin fara wani sabon zagayen tattaunawa.

Tun daga ranar 15 ga watan Afrilu, Sudan ke fama mummunan rikici tsakanin dakarun gwamnati da na RSF a Khartoum da sauran yankunan kasar. Alkaluman da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar, sun nuna cewa, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 3,000 tare da jikkatar wasu sama da 6,000.

A cewar hukumar kula da masu kaura ta MDD, kusan mutane miliyan 5.8 ne suka rasa matsugunansu a ciki da wajen Sudan, saboda tsawaitar rikicin. (Fa’iza Mustapha)