logo

HAUSA

Kimiyya ba dabarar takara ba ce

2023-10-26 16:10:47 CMG Hausa

Shahararriyar mujallar kimiyya da fasaha ta kasar Birtaniya “Nature” ta watsa wani bayani a shafinta na yanar gizo a kwanan nan cewa, kasar Sin a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, tana kokarin zurfafa hadin gwiwarta da sauran kasashe a fannin nazarin kimiyya da fasaha, da zummar daga matsayin wannan bangare a duk duniya. Kana a cikin bayanin, an yi kira ga kasashen Turai da kasar Amurka da su daina nuna son zuciya, su yi kokarin hada gwiwa da Sin a fannin kimiyya da fasaha, ta yadda za a taimaki dan Adam wajen tinkarar kalubalolin da suke fuskanta a fannonin siyasa, da tattalin arizki, da kuma muhalli.

Na yarda da ra’ayin marubucin wannan bayani, saboda ya nuna sanin ya kamata. Ko da yake yanzu a kasashen yamma, mutane su kan nuna tsattsauran ra’ayi a fannin siyasa, amma duk da haka marubucin ya bayyana gaskiya game da gudunmowar da kasar Sin ta samar wa bangaren kimiyya da fasaha na duniya. Kana hakan ya shaida cewa, nasarorin da kasar Sin ta cimma a wannan fanni, ba abun da za a iya boyewa ba ne.

A ra’ayin kasar Sin, tushen hulda da sauran kasashe shi ne, bude kofa, da ganin dukkan bangarori daban daban sun amfana. A bisa wannan ra’ayi ne, kasar Sin take kokarin hadin gwiwa da mabambantan kasashe don raya kimiyya da fasaha.

Ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2023, kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha tare da kasashe fiye da 80, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Kana kawancen kungiyoyin kimiyya na Ziri Daya da Hanya Daya, wanda ke da hedkwata a cibiyar nazarin kimiyya ta Sin, ya samar da tallafi ga mambobin kawancen 67 na kasashe 48 don su gudanar da ayyukan bincike.

Cikin shekaru 10 bayan gabatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya a shekarar 2013, kasar Sin ta gayyaci matasa masu nazarin kimiyya da fasaha fiye da dubu 10, daga kasashe daban daban zuwa kasar, don gudanar da aikin nazari da musayar ra’ayi, kana aka horar da kwararru masu fasahohi da jami’ai fiye da dubu 16. Ban da haka, Sin ta kafa dandalin mika fasahohi 9, a yankunan kudu maso gabashin Asiya, da kudancin nahiyar Asiya, da kasashen Larabawa, da nahiyar Afirka, da yankin Latin Amurka. Ta kuma taimakawa kasashe fiye da 50 dake nahiyar Afirka kafa cibiyar nuna fasahohin noma. Kana kasar ta yi hadin gwiwa da mabambantan kasashe wajen kafa dakunan gwajin fasahohi na Ziri Daya da Hanya Daya fiye da 50, wadanda suka shafi harkokin aikin noma, da sabbin makamashi, da kiwon lafiya, da dai sauransu. Sa’an nan, a wajen taron koli na hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na 3, da aka kawo karshensa a kwanan baya, kasar Sin ta tabbatar da cewa, za ta kara adadin dakunan gwajin zuwa 100, nan da shekaru 5 masu zuwa.

Sai dai idan mun duba matakan da wasu kasashen yamma ke dauka, za mu ga yadda suke hana ruwa gudu ga aikin hadin kan kasa da kasa ta fuskar kimiyya da fasaha. Inda su kan dauki matakin hana yaduwar fasahohi, da magance fitar da wasu kayayyakin fasahohi zuwa ketare, har ma ya kai ga neman gurgunta kamfanonin kimiyya da fasaha na sauran kasashe, da hana cudanyar kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha. A ganin wadannan kasashen, kimiyya da fasaha suna da matukar muhimmanci wajen takara da sauran kasashe, kana suna dogaro kan fasahohi masu ci gaba wajen kiyaye tsare-tsaren duniya na yanzu, da kare gibin dake tsakaninsu da mafi yawan kasashe ta fuskar tattalin arziki. Don haka, sam ba su son raba kimiyya da fasaha da sauran kasashe.

Wannan bambancin ra’ayi da ake samu tsakanin kasashen yamma da kasar Sin wani babban dalili ne da ya sa kasashen yamma kallon kasar Sin tamkar abokiyar gaba. Kasashen yamma na kokarin kare matsayinsu na jagorantar tattalin arzikin duniya, da mai tsara ka’idojin kasa da kasa, ta yadda za su iya more sakamakon ci gaban duniya su kadai. Amma kasar Sin ta ce, “Hakan bai yi daidai ba, ya kamata mu ba mabambantan kasashe damar cin moriya da samun ci gaba tare.” Wannan ra’ayi na Sin, a ganin kasashen yamma, tamkar raunana moriyarsu ta tushe ne.

Hakika kimiyya da fasaha sakamako ne na ci gaban al’ummar dan Adam, don haka ya kamata a yi amfani da su wajen amfanawa daukacin dan Adam, maimakon yin mummunar takara da su. Idan su ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa na kasashen yamma suka nuna sanin ya kamata, kamar yadda marubucin bayanin mujallar Nature ya yi, da tsara matakai bisa la’akari da moriyar daukacin dan Adam maimakon ta kansu kadai, tare da shiga cikin yunkurin kasar Sin na tabbatar da ci gaban duniya baki daya, to, tabbas za a samu ci gaban harkokin duniyarmu da daidaituwar al’amura cikin sauri. Sai dai ko za su iya yin haka? (Bello Wang)