logo

HAUSA

Wang Yi na kan hanyar zuwa Amurka domin yin shawarwari da jami’an kasar

2023-10-26 09:26:59 CMG Hausa

A yau ne, ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai isa birnin Washington na kasar Amurka, domin ganawa ta kwanaki biyu da gwamnatin Biden.

Kasashen Sin da Amurka na sake farfado da dangantakar da ta yi tsami a tsakaninsu, biyo bayan takaddamar harkokin kasuwanci da siyasa da ba a warware su ba.

Amma yanzu kasashe suna fatan yin aiki tare, don taimakawa wajen warware rikicin dake faruwa tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila.(Ibrahim)