logo

HAUSA

Isra’ila ta matsa kaimi wajen luguden wuta a Gaza yayin da ake fama da mummunar matsalar jin kai

2023-10-26 10:27:59 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da lafiya a Gaza dake karkashin kungiyar Hamas, ta ce adadin Falasdinawa da suka mutu sanadiyyar luguden wutan da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza, ya karu zuwa 6,546, yayin da wasu Falasdinawa 17,439 suka jikkata.

Wasu majiyoyi daga rundunar tsaron Falasdinu da wasu ganau, sun ce cikin kwanaki biyu da suka gabata, Isra’ila ta matsa kaimi wajen yin luguden wuta da harba makaman artillery a zirin Gaza.

Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, hare-hare ta sama da Isra’ila ke kaiwa yankin, sun ninka har sau uku idan aka kwatanta da kwanakin baya. (Fa’iza Mustapha)