logo

HAUSA

Sakataren MDD ya musanta zargin da ake yi masa na goyon bayan harin Hamas

2023-10-26 10:09:48 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kakkausar suka kan karyar da wasu manyan jami’an diflomasiyyar Isra’ila suka yi, wadanda suka zarge shi da goyon bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da kungiyar Hamas ta kai, a wata sanarwa da ya gabatar wa kwamitin sulhu.

Da yake jawabi a yayin muhawarar da kwamitin sulhu ya yi jiya, kan rikicin dake ci gaba da kazancewa a Isra'ila da Falasdinu, babban jami'in MDD ya ce, duk da cewa babu wani abu da zai iya zama hujjar munanan hare-haren da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wadanda suka haifar da kawanya da kaddamar da harin bama-bamai a Gaza, amma yana da muhimmanci a fahimci cewa, ba haka kawai suka faru ba, kuma ba hujja ce ta azabtar da Falasdinawa baki daya ba.

Bayan jawabin da Guterres ya yi a ranar Talata, zaunannen wakilin Isra'ila a MDD, Gilad Erdan ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa, jawabin Guterres ya nuna goyon bayan munanan harin na Hamas. Erdan ya bukaci babban jami'in MDD da ya yi murabus, daga bisani kuma ya ce, Isra'ila za ta hana jami'an MDD takardar iznin shiga kasar. (Ibrahim)