logo

HAUSA

A shirye Iran take ta hada gwiwa da Jamhuriyar Niger

2023-10-26 10:19:02 CMG Hausa

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya ce, a shirye Tehran take ta hada gwiwa da Niger a fannonin raya tattalin arziki.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na ofishin shugaban kasar Iran a jiya Laraba.

Ebrahim Raisi ya kuma bayyana yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Niger, Bakary Yaou Sangare a Tehran, babban birnin kasar cewa, cikin sama da shekaru 40 da suka gabata, Iran ta samu gogewa da karfi a fannoni daban-daban.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Niger, ya yabawa Iran bisa nasarorin da ta samu a bangarori daban-daban. Yana mai cewa, ziyarar da ya kai Tehran na da nufin inganta dangantakar abota tsakanin kasashen biyu tare da daga matsayin hadin gwiwar dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)