logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Rasha ba ta shafi wani bangare na uku ba

2023-10-26 09:17:13 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha ba ta shafi wani bangare na uku ba, kuma babu wani bangare na uku da zai dame ta.

Li ya bayyana haka ne, yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Rasha Mikhail Mishustin, a gefen taron majalisar shugabannin gwamnatocin mambobin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 22. Ya ce, bangarorin biyu suna gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu ne da nufin amfanar da jama'arsu, da inganta ci gaban duniya, da tabbatar da adalci da daidaito.

A nasa bangaren kuwa, Mishustin ya taya kasar Sin murnar samun nasarar karbar bakuncin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na uku. Yana mai cewa, hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Rasha da Sin a sabon zamani, ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba. (Ibrahim)