logo

HAUSA

Kasuwanci tsakanin Sin da Zimbabwe ya bunkasa

2023-10-25 10:14:03 CMG HAUSA

   

Ofishin jakadancin Sin dake kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, cinikayya tsakanin Sin da Zimbabwe a cikin watanni 9 na farkon bana, ya karu da kashi 39.4 cikin 100, zuwa dalar Amurka biliyan 2.43, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a shekarar da ta gabata, wanda ya zarce jimillar cinikin da aka yi a shekarar 2022.

A cewar ofishin jakadancin, darajar kayayyakin da Zimbabwe ta fitar zuwa kasar Sin a cikin wannan lokaci, ta kai dalar Amurka biliyan 1.36, yayin da darajar kayayyakin da aka shigo da su cikin kasar daga kasar Sin, ta kai dalar Amurka biliyan 1.07. Yana mai cewa, kayayyakin da kasar Sin ta ci gaba da shigo da su cikin kasar, sun taimakawa Zimbabwe wajen samun rarar cinikayyar da ta kai dalar Amurka miliyan 29.

A cewar hukumar kididdiga ta kasar Zimbabwe, a cikin watan Agusta, kasar Sin ta kasance kasa ta uku wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar Zimbabwe, inda makwabciyarta Afrika ta Kudu ta kasance a kan gaba, sai hadaddiyar daular Larabawa a matsayin babbar kasuwa ta biyu a fannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Dangane da shigo da kayayyaki kuwa, a watan Agusta, kasar Sin ta kasance babbar kasuwa ta biyu ga Zimbabwe, bayan Afirka ta Kudu. (Ibrahim Yaya)