Amurka ce ke rura wutar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila
2023-10-25 22:09:04 CMG
Daga Lubabatu Lei
Kawo yanzu, sama da mutanen Palasdinu da na Isra’ila 7200 suka halaka, sakamakon rikicin da ya barke a tsakaninsu tun ranar 7 ga wata. Duk da haka, John Kirby, babban jami’in kwamitin kula da harkokin tsaro na fadar White House ya bayyana cewa, “lokaci bai yi da za a tsagaita bude wuta”, dole ne Hamas ta saki fursunonin da take tsare da su tukuna. Ya yi furucin ne a lokacin da yake tattaunawa da tashar CNN a ranar 23 ga wata, inda ya ce, “Akwai sauran ayyuka ga Isra’ila wajen farautar jagororin kungiyar Hamas…Mu kuma za mu mai da hankali a kan tabbatar musu da dukkanin abubuwan da suke bukata wajen fadan.”
A yayin da rikici ke ci gaba da tabarbarewa tare da haifar da mutuwar dimbin fararen hula, tsagaita bude wuta abu ne da ya kamata a baiwa fifiko wajen tabbatar da shi, don haka ma galibin kasashen duniya na kira ga Palasdinu da Isra’ila da su dakatar da fada a tsakaninsu, amma ita kasar Amurka a maimakon haka, tana rura wutar rikicin, inda a kwanan nan, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta samar da dala biliyan 106, kuma daga cikin kudin, zai ware dala biliyan 14.3 ga Isra’ila a matsayin gudummawar soja. Baya ga haka, Amurka ta kuma tura jiragen ruwa masu daukar jiragen sama zuwa bahar Rum, tare da dada tura kayayyakin soja zuwa Isra’ila. Har ma sau biyu ne ta hana kwamitin sulhu na MDD zartas da daftarin kuduri da ya shafi batun Palasdinu da Isra’ila.
Kwanan nan, shehun malami a jami’ar Harvard, Stephan Walt, ya rubuta a mujallar Foreign Policy cewa, “Amurka ita ce sanadin sabon rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila.” Abin haka yake, Amurka ta dade tana mai da Isra’ila a matsayin makaminta a gabas ta tsakiya, don haifar da barazana ga Iran da sauran kasashen yankin, a sa’i daya kuma, kasancewar Yahudawan kasar Amurka suna yawan samar da kudade ga babban zaben kasar Amurka, wadanda ke da muhimmin tasiri ga harkokin siyasa na Amurka, don haka ne gwamnatin kasar Amurka take ta nuna goyon baya ga Isra’ila a rikicinta da Palasdinu, matakin da ya sa aka dade ana fuskantar matsalar Palasdinu da Isra’ila.
Kwanan nan, shugaba Biden ya gabatar da jawabi a wani shirin talabijin, inda bai ko boye ba ya ce, nuna goyon baya ga muhimman kawayen Amurka da suka hada da Isra’ila da Ukraine “jari ne da aka zuba da idon basira, wanda zai haifar da alfanu ga zuriyoyin Amurka”. A game da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova ta ce, “Kullum yake-yake na kasance ‘jarin da Amurka ta zuba da idon basira’, kasancewar bai faru a yankin Amurka ba, don haka ma ba su damu da hasarorin da suka haifar ga sauran kasashe ba.”
Lallai Amurka ta sha zancen hakkin dan Adam, amma kuma ta kawar da ido daga masifar jin kai da ke faruwa a Gaza, Amurka wadda take daukar kanta a matsayin mai rajin kare dimokuradiyya da hakkin dan Adam, amma kuma tana dora moriyar kanta a kan ta sauran kasashe da ma dokokin kasa da kasa.
Rikici na ci gaba a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wadda ke haifar da munanan hasarori ga fararen hula masu dimbin yawa. Sanyaya yanayin da ake ciki da ma magance hasarar rayukan fararen hula shi ne ainihin abin da ya kamata a yi wajen kare hakkin bil Adam. Kasashen duniya, musamman ma manyan kasashe, ya kamata su taka rawar da ta kamata, su dauki matakan da suka wajaba na sa kaimin yin shawarwari da dakatar da bude wuta, don maido da zaman lafiya tun da wuri.(Mai Zane: Mustapha Bulama)