logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci da a tsagaita bude wuta tsakanin Falasdinu da Isra'ila

2023-10-25 10:46:01 CMG HAUSA

 

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya yi kira da a tsagaita bude wuta tsakanin Falasdinu da Isra'ila.

Zhang Jun ya bayyana haka ne, yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, ciki har da batun Palasdinawa. Yana mai cewa, shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, tilas ne a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba. Kuma wannan shi ne kiran da kasashen duniya suka yi.

Ya ce, saboda dimbin kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi, wajibi ne majalisar ta yi amfani da kalaman da suka dace wajen neman tsagaita bude wuta cikin gaggawa.

Wakilin na Sin ya kara da cewa, dole ne a fahimci cewa, barin fadan da ake yi a Gaza ya ci gaba da ma kara rura shi kan kowace irin hujja, ba zai haifar da cikakkiyar nasarar soji ga kowane bangare ba, sai ma ya haifar da wani bala'i da zai mamaye da ma yin kaca-kaca da yankin baki daya, kuma hakan ka iya dakushe fatan da ake da shi na kafa kasashe biyu, da kuma jefa al'ummar Palasdinu da Isra'ila cikin wani mummunan yanayi na kiyayya da yin fito na fito. (Ibrahim Yaya)