logo

HAUSA

Jakadan Sin mai kula da shirin kwance damarar makamai ya yi kira da a tabbatar da ikon kasashe masu tasowa na yin amfani da kimiyya da fasaha cikin lumana

2023-10-25 10:29:21 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin dake aikin kwance damarar makamai Shen Jian, ya gabatar da jawabi a kwamitin kula da kwance damara da tsaron kasa da kasa na babban taron MDD karo na 78, a madadin kasashe 24 da suka gabatar da kudurin “kara azama kan yin hadin gwiwar kasa da kasa cikin ruwan sanyi a fannin tsaron kasa da kasa”, inda ya yi kira da a tabbatar da ‘yancin kasashe masu tasowa na yin amfani da kimiyya da fasaha cikin lumana.

Shen Jian ya bayyana cewa, a sabon zamanin da muka ciki, yin amfani da kimiyya da fasaha cikin lumana, ya zama muhimmin abu ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa, kana ba za a kau da kai daga tasirin da bunkasuwar kimiyya da fasaha ta kawo wa tsaron duniya ba. Kasashen da suka gabatar da kudurin sun yi maraba da kasa da kasa da su yi alkawari tare da yin kokari tare don sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta fuskar kimiyya da fasaha cikin lumana, da samun ci gaban hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban. Ya kamata kasashen duniya su dauki matakai masu inganci don aiwatar da kudurin yin amfani da kimiyya da fasaha cikin lumana, ta hakan za a tabbatar da ikon kasashe masu tasowa a wannan fanni. (Zainab)