logo

HAUSA

Mata na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa

2023-10-25 07:57:37 CMG Hausa

A ranar Litinin 23 ga wata ne aka bude babban taron wakilan mata na kasar Sin karo na 13 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Jagororin kasa da na Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), ciki har da Xi Jinping sun halarci bikin domin taya matan murna.

Ding Xuexiang, mamban zaunanen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin, ya gabatar da jawabi a madadin kwamitin kolin JKS, inda ya taya murnar bude taron, tare da mika gaisuwar ban girma ga mata dake kokarin ingiza ci gaban mata a fadin kasar, da ’yan uwa mata na yankunan musamman na Hong kong da Macao, da kuma Taiwan, da matan Sinawa mazauna kasashen waje.

Ya kuma bayyana irin gagarumar gudunmawar da matan kasar Sin suka bayar tun bayan babban taron wakilan mata na kasar karo na 12 da aka shirya yau shekaru 5 da suka gabata. Inda ya yi kira ga mata a fadin kasar Sin, da su kara zage damtse tare da kokarin sauke nauyin dake wuyansu a wannan sabuwar tafiya.

Kimanin wakilan mata 1,800 ne suka halarci taron, baya ga wakilai 90 da aka gayyata na musamman daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao.

Bayanai na nuna cewa, mata a fannonin daban-daban kamar takwarorinsu maza, na bayar da gagarumar gudummawa wajen ciyar da kasar Sin gaba a dukkan fannoni. Matakin dake kara fito da sunayen mata a wasu fagage, kamar kasuwanci da ilimi da harkokin mulki da diflomasiya, da binciken sararin samaniya da bangaren tsaro da aikin soja da ’yan sanda da kwastam da sauransu.  Wannan a cewar masu fashin baki, ya faru bisa jerin manufofi da tsare-tsare da mahukuntan kasar Sin suka bullo da su don ganin ana damawa da mata a fannoni daban-daban na raya kasa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)