logo

HAUSA

CMG da AFP sun kaddamar da sabon zagayen hadin-gwiwa

2023-10-25 21:27:12 CMG Hausa

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG a takaice, da kamfanin dillancin labarai na AFP ta kasar Faransa, sun kaddamar da hadin-gwiwa a sabon zagaye. Yau Laraba 25 ga wata ne, mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong, da shugaban kamfanin AFP, Fabrice Fries, suka rattaba hannu kan takardar bayanin hadin-gwiwa a birnin Paris.

Bisa yarjejeniyar, bangarorin biyu za su yi amfani da damar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a Paris domin karfafa hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi sabbin kafafen yada labarai da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da habaka hadin-gwiwa daga dukkan fannoni. (Murtala Zhang)