logo

HAUSA

Mambobin BRICS sun amince da zurfafa hadin gwiwa domin farfado da bangaren yawon bude ido

2023-10-25 10:33:59 CMG HAUSA

 

Kasashen kungiyar BRICS sun amince da kara zurfafa hadin gwiwa domin samun farfadowar bangaren yawon bude ido ta kowacce fuska tare da dorewarsa.

Kungiyar kasashe 5 masu samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri da suka hada da Brazil da Rasha da India da Sin da Afrika ta kudu, ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar bayan taron da ministocin kula da yawon bude ido na kasashenta suka yi a birnin Cape Town na Afrika ta Kudu a jiya Talata.

Sanarwar ta ruwaito kasashen BRICS sun bayyana mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar ga bangaren yawon bude ido. Sai dai, sun yi imanin cewa, annobar ta samar da damar aiwatar da sauye-sauye yayin da bangarorin tafiye-tafye da na yawon bude ido ke da kyakkawar makoma mai juriya.

Har ila yau, ta ruwaito ministocin na yin maraba da gayyatar da kungiyar ta mikawa kasashen Argentina da Masar da Habasha da Saudiyya da Hadaddiyar daular Larabawa domin zama mambobinta daga ranar 1 ga watan Junairun 2024. (Fa’iza Mustapha)