logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya isa Kyrgystan domin taron SCO

2023-10-25 10:24:33 CMG HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Bishkek, fadar mulkin kasar Kyrgystan a jiya Talata, domin ziyarar aiki da halartar taro karo na 22 na shugabannin gwamnatocin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), wanda zai gudana daga jiya Talata zuwa Juma’a.

Yayin da yake ganawa da Akylbek Japarov, takwaransa na Kyrgyzstan a filin jirgin sama, Li Qiang ya ce, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da Kyrgyzstan wajen aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da zurfafa aminci kan harkokin siyasa da manufofi da samar da sabbin hanyoyin hadin gwiwa da bunkasa dangantakar abota a tsakaninsu.

Ya kara da cewa, bangaren Sin na sa ran hada hannu da sauran mambobin SCO wajen daukaka ruhin Shanghai da ingiza sabon kuzari ga zaman lafiya da kwaciyar hankali da ci gaban yankinsu. (Fa’iza Mustapha)