Kashim Shettima: Najeriya na tare da kasar Sin a duk abun da zai kawo bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya ga al’ummarta
2023-10-24 15:23:09 CMG Hausa
Kwanan nan ne mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Kashim Shettima ya shigo Beijing, fadar mulkin kasar Sin, don halartar babban dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na uku, wato BRI a turance.
A zantawarsa da ‘yan jaridun sashen Hausa na CMG, Kashim Shettima ya ce, inganta hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wajen raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, na da babbar ma’ana da muhimmanci ga bangarorin biyu, ciki har da kyautata muhimman ababen more rayuwar al’umma a tarayyar Najeriya.
Kana, Kashim Shettima ya yaba da wasu manyan shawarwari uku da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da su, wadanda suka shafi ci gaba, da tsaro gami da al’adu na duk fadin duniya.
A karshe, Kashim Shettima ya ce, kasarsa na fatan yin kokari tare da kasar Sin, domin bayar da gudummawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka da ma duk duniya baki daya. (Murtala Zhang)