logo

HAUSA

Mohanad Ali Moh’d Shalabi: Ina Masa Godiya Da Ba Ni Damar Samun Nasara!

2023-10-24 08:29:26 CMG Hausa

Mohanad Ali Moh’d Shalabi, dan kasuwa ne da ya fito daga kasar Jordan, yana tafiyar da wani dakin cin abinci a birnin Yiwu na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin. Isowarsa Zhejiang ke da wuya, sai ya yi fatan yin kasuwanci a kasar Sin.

A watan Yunin shekarar 2014 ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana labarinsa na yin aiki tukuru, a yayin taron dandalin tattaunawar kasar Sin da kasashen Larabawa, inda ya ce, wani matashin dan kasashen Larabawa ya sanya burinsa cikin mafarkin kasar Sin wanda al’ummar Sin ke kokarin cimmawa. Yana aiki tukuru, lamarin da ya nuna hadewar mafarkin kasar Sin da mafarkin kasashen Larabawa.

Mohanad ya zana hoton “Ziri Daya da Hanya Daya” a jikin bangon dakin cin abincinsa. Ya yi wa shugaba Xi godiya sosai. Ya kuma yaba da ma aika bidiyo da yawa dangane da shugaba Xi ga abokansa. Ya ce, kasar Sin mai bude kofa ga kowa ta bai wa baki damammaki da yawa, ta kuma taimaka masa cimma burinsa. (Tasallah Yuan)