logo

HAUSA

Me ya sa dangantaka da Sin ke samun karbuwa a Afrika?

2023-10-24 17:22:25 CMG Hausa

Baki sama da 300 daga Sin da kasashen Afrika 53 ne suka tattauna a jiya Litinin game da gudanar da taron dandalin FOCAC na badi.  

Dandalin FOCAC dai ya kasance muhimmiyar laima da kasashen Sin da Afrika ke hadin gwiwa karkashinta, wanda kuma ke samun karbuwa matuka tsakanin kasashen Afrika.  Shin me ya sa dangantaka da Sin ke kara samun karbuwa a Afrika?

Saboda kasar Sin ta zo da sabuwar dabarar hadin gwiwa da ba a saba gani ba. Wato mutuntawa da girmawawa da moriyar juna. A baya, hadin gwiwa da kasashen Afrika ke yi da iyayen gidansu, ta kasnace bisa wasu sharudda da wadancan kasashe ke gindayawa ko kuma ci da gumin kasashen da kwashe albarkatunsu. Amma a yanzu, ba haka abun yake ba, kasashen Afrika sun san darajar kansu saboda yadda kasar Sin ke daukarsu a matsayin ’yan uwanta ba tare da nuna iko ko fifiko ba.

Abu na biyu shi ne, kasar Sin tana fada da cikawa. Wato tana samar da tarin damarmaki tare da cika alkawuranta. Na yi imanin cewa, irin alfanun da kasashen suka samu daga hadin gwiwarsu da Sin a kankanin lokaci, bai kai abun da suka samu daga iyayen gidansu masu mulkin mallaka ba. Babu inda kasar Sin ba ta taba ba a fannonin rayuwar al’umma, kama daga ababen more rayuwa zuwa tsaro da kasuwanci da fasahohi da sauransu. Ba za a iya taba raba ci gaban da kasashen Afrika suka samu cikin sauri ba da taimakon kasar Sin.

Abu na 3 a ganina shi ne, yadda kasar Sin ta samarwa kasashen Afrika damar bayyana ra’ayinsu. Bisa yadda take tafiyar da dangantakarta da su, yanzu kasashen Afrika sun san abun da ya dace da su, da yadda za su kwaci kansu. Yayin wani taro da aka gudanar tsakanin kasashen Afrika da na Turai a kwanakin baya, na ji shugaban wata kasa a Afrika na cewa, lallai ya kamata a rika daukarsu da muhimmanci. Kuma kamata ya yi a rika ba su dama kamar sauran manyan kasashe. Wannan tamkar nanata kira da kokarin da kasar Sin ne na ganin duniya ba ta kasance karkashin ikon wata kasa ko wasu tsiraru ba.

Hakika kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai da ci gaban kasashen Afrika. (Faeza Mustapha)