logo

HAUSA

’Yan bindiga sun hallaka mutane 5 tare da sace wasu 5 a jihar Katsina

2023-10-24 10:19:17 CMG Hausa

A kalla mutane 5 ne wasu ’yan bindiga suka hallaka, baya ga wasu karin mutane 5 da suka yi awon gaba da su, yayin wani farmaki da suka kaiwa garin Danmusa, fadar mulkin karamar hukumar Danmusa dake jihar Katsina ta arewa maso yammacin Najeriya.

Da yake tabbatar da aukuwar harin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho a jiya Litinin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Abubakar Sadik, ya ce maharan sun aukawa garin na Danmusa ne da daren ranar Lahadi, inda suka rika harbin kan mai tsautsayi.

Abubakar Sadik, ya kara da cewa, rundunar ’yan sanda ta baza jami’ai domin farautar maharan, da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, kuma za su gudanar da bincike game da aukuwar harin.

A watannin baya-baya nan, hare-haren ’yan bindiga na cikin manyan kalubalen tsaro da ake fama da su a yankin arewa da tsakiyar Najeriya, wanda sau da dama kan haifar da asarar rayuka, da kuma garkuwa da mutane. (Saminu Alhassan)