Kutsen da wasu jiragen ruwan Philippines suka yi a Ren’ai Jiao dake tekun kudancin kasar Sin ya bayyana makircin Amurka
2023-10-24 21:06:12 CMG Hausa
Kwanan nan ne, wasu jiragen ruwan kasar Philippines guda hudu, ciki har da jiragen ruwan dakon kaya 2 gami da jiragen ruwan ‘yan sandan tsaron teku 2, suka shiga cikin yankin ruwan dake dab da Ren’ai Jiao na tsibiran Nansha na kasar Sin, ba tare da samun izini daga gwamnatin kasar ba, tare kuma da cin karo da jirgin ruwan ‘yan sandan tsaron tekun kasar Sin gami da jirgin ruwan kamun kifi na kasar. Har ila yau, kasar Philippines ta zargi kasar Sin da cewa, wai Sin ta rura wutar rikici da gangan, kana, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa, inda ta zargi halastaccen matakin da kasar Sin ta dauka daidai bisa doka. Wannan tamkar makirci ne da Philippines da Amurka suka kulla tun tuni.
Tun farkon shekarar da muke ciki, Philippines tana daukar matakai iri-iri kan batun tekun kudancin kasar Sin, inda sau da dama ta yi kutse cikin yankin tekun dake dab da tsibirin Huangyan da Ren’ai Jiao, a wani yunkuri na hura wutar rikici. Masanan dake binciken batutuwan kudu maso gabashin nahiyar Asiya sun bayyana cewa, Amurka ce take goya wa Philippines baya. A halin yanzu, Amurka tana gaggauta aiwatar da “tsare-tsaren tekunan Indiya da Pasifik”, da nufin takawa ci gaban kasar Sin birki, kuma kasashen dake yankin kudu maso gabashin Asiya na da muhimmanci sosai ga tsare-tsaren Amurka. A baya-bayan nan ne, wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka suka ziyarci kasashen kudu maso gabashin Asiya, da zummar tilasta musu yin zabi tsakanin Sin da Amurka, da bata dangantakarsu da kasar Sin bisa batun tekun kudancin kasar Sin, da illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. (Murtala Zhang)