logo

HAUSA

An kai kayayyakin agaji karo na 3 cikin yankin Gaza

2023-10-24 10:31:29 CMG Hausa

Wasu manyan motoci 20 dauke da kayayyakin agaji, sun shiga yankin Gaza, bisa kan iyakar mashigar Rafah. Kayayyakin wadanda aka shigar Gaza a jiya Litinin su kasance irinsu jeri na 3 da aka kai cikin yankin, ta Rafah dake kan iyakar Falasdinu da kasar Masar.

Wata majiya daga bangaren Falasdinu ta ce, kayayyakin agajin sun hada da magunguna, da kayan aikin jinya, da abinci, gami da ruwa. Kana hukumar kula da aikin kai dauki ga ’yan gudun hijira dake yankin gabas maras nisa, da Falasdinu, ta Majalisar Dinkin Duniya, za ta sa ido kan aikin jigilar kayayyakin agajin. (Bello Wang)