logo

HAUSA

An yi taro na 4 na dandalin Abuja

2023-10-24 11:31:34 CMG Hausa

A ranar 19 ga watan nan ne aka gudanar da taro na 4, na dandalin tattaunawa na Abuja, a cibiyar albarkatun aikin soja ta Najeriya, wadda ke birnin Abuja, fadar mulkin kasar.

Bangarorin da suka karbi bakuncin taron sun hada da cibiyar nazarin Afirka ta jami’ar ZNU ta kasar Sin, da cibiyar bincike ta Gusau dake Najeriya. Kana jami’ai, da masana, da wakilan kamfanoni na bangarorin 2, da yawansu ya kai fiye da 100, sun halarci taron, mai taken “ Aiwatar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, don tabbatar da ci gaban nahiyar Afirka da kasar Sin a sabon zamani”, kana an yi tattaunawa mai zurfi.

Yayin da yake ba da jawabi a wajen taron, jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya ce taron dandalin kolin hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), wanda ya gudana a birnin Beijing na Sin a kwanan baya, ya samar da dimbin sakamako, wadanda za su amfani dukkan kasashen, da kungiyoyin da suka halarci shawarar BRI, gami da daukacin duniya baki daya. Kana a nata bangare, kasar Sin na kara kokarin taka muhimmiyar rawa, wajen aiwatar da shawarar BRI cikin inganci.

A nasa bangare kuwa, tsohon ministan tsaron kasar Najeriya Aliyu Gusau Mohammed, cewa ya yi, kamata ya yi a tsara sabon tsarin hadin gwiwa, tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, don tinkarar kalubalolin da ake fuskanta a duniyarmu, da samar da gudunmawar hadin kai, ga yunkurin tabbatar da tsare-tsaren kasa da kasa, wadanda za su iya haifar da kwanciyar hankali, da kulawa da moriyar sassa daban daban. (Bello Wang)