logo

HAUSA

Kungiyar Hamas ta saki wasu ’yan Isra'ila mata tsoffi 2

2023-10-24 10:34:46 CMG Hausa

A jiya ne, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Palasdinawa wato Hamas, ta saki wasu mata tsoffi guda biyu da ta yi garkuwa da su a zirin Gaza, yayin da wasu karin jiragen sama dauke da kayayyakin jin kai suka sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Al-Arish dake arewacin Sinai, na kasar Masar, inda ake jiran aika su zuwa Gaza da yaki ya daidaita.

Kungiyar baradin Al-Qassam, reshen soji na Hamas, ta fada jiya Litinin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, ta kara sakin wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su, bisa dalilai na jin kai ta hanyar shiga tsakanin kasashen Masar da Qatar.

Wannan shi ne karo na biyu da Hamas ta saki wasu daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, bayan ta sako wasu Amurkawa biyu a ranar Juma'ar da ta gabata.

Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya tabbatar da sakin ’yan Isra'ilan biyu da suka isa mashigar Rafah dake tsakanin Gaza da Masar. Yana mai cewa, wata tawagar Isra'ila na kan hanyarta ta ganawa da su. (Ibrahim Yaya)