logo

HAUSA

Sojojin Sudan sun bayyana aniyar komawa teburin shawara a Jeddah

2023-10-23 10:18:35 CMG HAUSA

 

Sojojin gwamnatin Sudan sun ce a ranar Alhamis mai zuwa za su koma teburin shawara tare da dakarun ko-ta-kwana na kasar ko RSF, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Da yake karin haske ga sojojin rundunar SAF kan hakan, a sansanin soji na Wadi Seidna dake birnin Omdurman, mataimakin kwamandan rundunar Shams-Eddin Kabashi, ya ce, "Mun samu gayyata zuwa tattaunawa a Jeddah, kuma tawagarmu za ta isa birnin na Jeddah domin fara shawarwari tun daga ranar Alhamis."

Wata kafar watsa labarai ta Sudan ta rawaito cewa, masarautar Saudiyya da Amurka, wadanda suke shiga tsakanin sassan biyu tun daga watan Mayu, su ne suka sake ayyana ranar komawa teburin tattaunawar. Kafin hakan, an dakatar da zaman sulhu ne tun cikin watan Yuli, saboda wasu batutuwa manya, da suka haifar da sabani tsakanin bangarorin sojin biyu na kasar Sudan.

Dakarun SAF da na RSF sun fara dauki ba dadi da juna ne a birnin Khartoum, da wasu karin sassan kasar tun daga ranar 15 ga watan Afirilun bana, wanda hakan ya haifar da kisan a kalla mutane 3,000, baya ga wasu sama da 6,000 da suka ji raunuka, kamar dai yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana.

A daya bangaren kuma, hukumar MDD mai lura da ’yan gudun hijira, ta ce kusan ’yan kasar ta Sudan miliyan 5.8 ne suka rasa matsugunan su a ciki da wajen kasa, sakamakon tsawaitar lokacin da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin dakarun na SAF da RSF. (Saminu Alhassan)