Mata Sinawa na dukufa wajen yada wasan Kungfu a kasashen waje
2023-10-23 16:21:43 CMG Hausa
Fasahar dambe irin na martial arts na kasar Sin, wanda kuma aka sani da wasan kungfu ko wushu na kasar Sin, wani muhimmin bangare ne na al'adun gargajiya na kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan, Sinawa da yawa a ketare sun bude makarantu da kafa kulake don koyar da fasahar wasan Kungfu. Wasan na kasar Sin, na da dogon tarihi cike da al'adun gargajiya, ya kuma jawo hankalin jama'a sosai, don haka ya zama wata hanya mai muhimmanci ta yadda baki ke fahimtar al'adun Sinawa.
Chang Chun ‘yar asalin lardin Henan ce na tsakiyar kasar Sin. Ta fara koyon fasahar wasan Kongfu a makarantar wasan ta Shaolin Tagou, dake birnin Dengfeng na lardin Henan, a shekarar 2004. Haikalin Shaolin, ko Shaolin Temple, na Dengfeng, shi ne abu mafi sha'awa ga gungun masoya Kungfu masu tasowa a duk duniya.
Bayan ta yi nazari na kusan shekara guda, ta bar makarantar don ci gaba da karatu a makarantar yawon bude ido da ke Zhengzhou, babban birnin lardin.
Wata rana, lokacin da ta koma makarantar wasan Kungfu ta Shaolin Tagou, don ziyartar malamanta da abokanta, ta sadu da Matthew, wanda ke da suna Bai Long a Sinance, daga Burtaniya, wanda ya je Sin don koyon fasahar a makarantar. Bisa la'akari da sha'awar da suke da ita game da wasan Kungfu, Chang Chun da Bai Long sun zama abokai na kwarai, kuma daga bisani sun yi soyayya.
Sun kaura zuwa London a shekara ta 2008, kuma daga karshe sun kafa makarantar koyar da fasahar wasan Kungfu. Chang Chun ta ce, "A Burtaniya, wasan Kungfu bai shahara ba idan aka kwatanta da wasan taekwondo, karate da sauran wasanni, kuma akwai karancin masu kallo. Ina ganin muna da damar samun ci gaba, kuma akwai alhakin yada al'adun Shaolin da ruhin Kungfu a kanmu. Galibi dalibanmu ‘yan Birtaniya ne, amma akwai wasu daga wasu kasashe. Muna kuma koyar da kwasa-kwasai ta yanar gizo." Ita da Bai Long sun yi aure a shekara ta 2009. Suna da ɗa, wanda ke koyon wasan Kungfu, karkashin jagorancinsu.
Shekaru uku da suka wuce, wata uwa ta shigar da diyarta mai watanni 18 makarantar, wanda hakan ya bai wa Chang Chun da Bai Long mamaki. "A yadda aka saba, muna daukar dalibai masu shekaru 4 ko sama da haka. Yarinyar ta yi kankantar shiga azuzuwan horo na yau da kullun. Don haka muka bude ajujuwa na musamman don biyan mabambantan bukatu na dalibanmu," in ji Chang Chun. Yarinyar ta kan yi kuka lokacin da ta fara koyon wasan Kungfu, amma sannu a hankali wasan ya fara shigar jikinta. Yanzu, yarinyar ta mai da hankali kan koyo sosai, kuma ta dauki makarantar a matsayin gidanta na biyu. Bidiyoyin yadda take nuna fasaharta ta wasan Kungfu sun dauki hankalin jama’a da yawa a shafukan sada zumunta.
Wani dalibi da ya yi nazarin wasan Kungfu fiye da shekaru 10 ya burge Chang Chun. Chang ta gabatar da cewa, “dalibin ya kan yi tafiyar sa'o'i hudu a kowane mako don halartar wani horo na awa daya a makarantarmu. Sama da shekaru 10 da suka wuce, ya kusa yanke kauna da rayuwa bayan mutuwar dansa ba zato ba tsammani. Ya samu labarin makarantarmu a lokacin wani aiki, daga bisani ya kamu da soyayyar wasan Kungfu a ajinsa na farko. A yayin koyon wasan, sannu a hankali ya sake samun karfin gwiwa game da rayuwa."
Bai Long ya ja hankalin kafofin watsa labarai da dama, ta hanyar fitowa a shirye-shiryen talabijin na gaskiya, inda ya koyar da matasan Birtaniya dabarun kare kai da kuma falsafar fasahar wasan Kungfu na kasar Sin. Chang ta ce, "ko a yanzu, wasu masoyana suna yin tsokaci a shafina na dandalin sada zumunta, suna cewa shirin kwaikwayo na gaskiya ya burge su. Mijina ya kasance yana yin wasan Kungfu tun yana dan shekara 11. Fasahar wasan ita ce soyayyar rayuwarsa."
He Wenyan, wadda ta fara wasan Kungfu tun tana ‘yar shekara 4, a baya kwararriyar ‘yar wasan ce a kasar Sin. A shekarar 2015, ta koma birnin Berlin na kasar Jamus, inda ta koyar da fasahar wasan Kungfu na kasar Sin a wani kulob ɗin wasan. A lokacin, He ta kulla abota da wata dalibar wasan Kungfu daga kasar Canada. Daga baya, sun kafa kungiyar wasan Kungfu, mai suna Wuhun, wanda a zahiri ke nufin ruhun wasan Kungfu.
A lokacin da ta tattauna da dalibarta ‘yar kasar Canada, He ta ce, “ita ce dalibar da ta fi burge ni, shekaru da dama da suka wuce na koma kasar Sin da zama na wasu watanni, ta biyo ni zuwa kasar Sin, kuma ta yi nazari a wani kulob ɗin wasan Kungfu a Yangshuo, dake lardin Guangxi na kabilar Zhuang mai cin gashin kansa a kudancin kasar Sin, na wani dan lokaci, wannan shi ne karon farko da ta ziyarci kasar Sin, kuma tana kaunar al'adun kasar Sin, yanzu tana iya yin mu'amala da ni cikin Sinanci mai sauki."
He ta fi koyar da wasan Kungfu irin na gasa. Ta ce, "idan aka kwatanta da wasan Kungfu na gargajiya, salon wasan na gasa na musamman ya fi bayyana. Dalibai za su iya shirya motsin jiki na wasan bisa yadda suke so. Tsarin yana kama da koyon rawa."
He na da yakinin cewa yin nazarin fasahar wasan na taimaka wa dalibai su karfafa jajircewarsu, kuma yana taimaka musu su kara kwarin gwiwa. A cikin karamin ajin kulob din, yara sun fi mayar da hankali a kan koyon fasahohi na asali, kamar danna kafafu, shuri da kuma tsayuwan hawan doki. Wani lokaci su kan yi kuka saboda kafafunsu sun yi zafi yayin da suke daukar horo, amma ko yaushe He na karfafa wa yaran gwiwa.
"Kin ga, Malama He, Yanzu na samu kwarewa fiye da yadda nake a baya," yaran su kan gaya wa He, cikin farin ciki, a duk lokacin da suka samu ci gaba. He ce, "ina gaya musu ni ma na kan zubar da hawaye a wasu lokuta idan na zurfafa yin horo. Amma abin da ya fi dacewa shi ne kuna iya kammala aikin duk da kukan da kuke yi. Abin farin ciki ne ganin yaran suna samun ci gaba."
A shekarar 2022, an gayyaci He halartar wani biki, wanda kungiyar Sinawa mazauna Berlin ta shirya, domin murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Jamus. Wasan Kungfu na He ya burge masu kallo. Mutane da yawa sun tashi tsaye daga kujerunsu suna jinjina mata, kuma mutane da yawa sun nemi bayanin tuntubar He.
"Kafin wasa na, yara shida daga kulob ɗina sun yi wasan Kungfu a kan dandamali. Sun cire tsoro a zuciyarsu duk da cewa wannan ne wasansu a karon farko, kuma sun gabatar da kyakkyawan wasa." in ji He. (Kande Gao)