logo

HAUSA

Ayarin motocin agaji na biyu na kan hanyar zuwa Gaza ta mashigar Rafah

2023-10-23 10:15:13 CMG HAUSA

 

Jami’an agaji dake kan iyakar Rafah sun bayyana cewa, wasu ayarin motocin dakon kaya guda 17 dauke da kayan agaji, sun isa iyakar Rafah dake yankin kasar Masar jiya Lahadi, kafin su nufi yankin zirin Gaza da ke fama da matsalar jin kai, biyo bayan hare-hrane da Isra’ila ke kaiwa.

Wannan shi ne ayarin motocin agaji na biyu da aka aika zuwa Gaza, bayan da ayarin farko na manyan motoci 20 da ke dauke da kayayyakin jin kai, sun shiga yankin da aka yiwa kawanya ranar Asabar.

Kayayyakin agajin na jiya ya kunshi abinci, da kayayyakin jinya, da ruwa, da barguna, da tufafi, da likkafani, da sauran kayayyaki, kamar yadda Ra'ed el-Gebaly, wani mai aikin sa kai a kungiya mai zaman kanta dake tattara abincin taimako ga mabukata a Masar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen mashigar Masar.

Masu aikin agaji sun bayyana cewa, motocin da kungiyar National Alliance for Civil Development Work, hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu na Masar, tare da hadin gwiwar kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Masar suka shirya, an tsara mika su ne ga masu aikin jin kai na MDD, da kungiyar Red Crescent ta Palasdinawa, da kuma Kungiyar agaji ta Red Cross a bangaren Gaza. (Ibrahim Yaya)