logo

HAUSA

Motsa jiki na tsawon minti 11 a ko wace rana na taimakawa rage hadarin mutuwar wuri (B)

2023-10-23 09:11:50 CMG Hausa

 

Masu karatu, yau bari mu ci gaba da tattauna batun motsa jiki.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta shawarci baligai su motsa jiki bisa matsakaicin karfi a kalla mintoci dari 1 da 50 ko kuma bisa babban karfi a kalla mintoci 75 a ko wane mako.

To, mene ne ma’anar motsa jiki bisa matsakaicin karfi? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, yayin da mutane suke motsa jiki bisa matsakacin karfi, bugun zuciya kan yi sauri, a kan yi gumi kadan, a yi numfashi da sauri kadan, amma ana maganar yadda ya kamata.

A shirinmu na makon jiya, masu nazari sun ce, wadanda ba sa motsa jiki kullum sun ji dadin sakamakon nazarinsu sosai, wato motsa jiki na tsawon minti 11 a ko wace rana na taimakawa rage hadarin mutuwar wuri. Za su fara motsa jiki ne daga motsa jiki kadan a ko wace rana. Abu mai sauki da za su yi shi ne motsa jiki cikin mintoci 10 da wani abu a ko wace rana. Ba sa bukatar zuwa dakin motsa jiki. Alal misali, yayin da suke kan hanyar zuwa wurin aiki, to, su sauka daga mota kafin su isa wurin aikin, su yi tafiya da kafaffu, ko su hau keke, akwai hanyoyi daban daban da za su bi wajen motsa jiki.

Amma masu nazarin sun yi nuni da cewa, akwai rauni dangane da nazarinsu, wato a kan dauki shekaru da dama ana nazarin alakar da ke tsakanin motsa jiki da kuma hadarin kamuwa da cututtukan da ke addabar mutane cikin dogon lokaci, an gudanar da nazarce-nazarcen ne yau shekaru fiye da 10 da suka wuce, inda wadanda aka yi bincike kansu suka sanar da yadda suke motsa jiki da kansu, amma idan sun sanya agogon motsa jiki da sauran na’urorin motsa jiki, to, za a samu bayanai masu inganci.

Ciwon zuciya, shan inna da sauran cututtukan da suka shafi jijiyoyin zuciya, muhimman dalilai ne da suke haddasa mutuwar mutane a duniya. A shekarar 2019 ne mutanen da yawansu ya kai miliyan 17 da dubu 900 suka rasa rayukansu sakamakon wadannan cututtuka a duk duniya. A shekarar 2020 kuma, ciwon kansa ya haifar da mutuwar mutane kusan miliyan 10 a duk duniya. (Tasallah Yuan)