Tashar Lekki na taimakawa Nijeriya wajen kara yin mu’amala da kasashen waje
2023-10-23 11:40:38 CMG Hausa
Masu kallonmu, barkanmu da war haka! Tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki da kasashen Sin da Nijeriya suka gina cikin hadin gwiwa, ta zama daya daga cikin sakamakon da aka cimma bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”. A halin yanzu, tashar na taimakawa Nijeriya wajen karfafa mu’amala a tsakaninta da kasashen duniya, kuma ana sa ran tashar za ta kasance cibiyar cinikayya a duk fadin nahiyar Afirka cikin shekaru da dama masu zuwa.