logo

HAUSA

Najeriya ta kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinta da Nijar sakamakon janyewar dakarun Faransa daga kasar

2023-10-23 09:43:39 CMG HAUSA

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara daukar matakan tsaro a kan iyakokinta da jamhuriyyar Nijar sakamakon janyewar da dakarun Faransa za su yi daga kasar, nan da karshen watan Disambar wannan shekara.

A lokacin da ya ziyarci jami’an hukumar kwastam a iyakar Maigatari dake jihar Jigawa a arewacin Najeriya, babban jami’in hukumar kwastam mai lura da jihohin Kano da Jigawa Alhaji Dauda Ibrahim ya ja hankalin daukacin ma’aikatan dake kula da iyakoki da su kara jan damara.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.