logo

HAUSA

TEPCO: An gano wasu gurbataccen sinadari cikin ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima da za a zubar a teku a zagaye na uku

2023-10-22 17:12:47 CMG

Kashi na uku na ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima da Japan ta shirya zubawa a teku a zagaye na uku na dauke da gurbataccen sinadarin radionuclides da ya hada da carbon-14, cobalt 60, strontium-90 da dai sauransu, bisa ga sakamakon gwajin farko da aka yi da kamfanin wutan lantarki na Tokyo ko TEPCO a takaice ya fitar.

Duk da nuna damuwa da adawa daga masunta na cikin gida da ma na sauran kasashe, TEPCO ta ce za a fara shirye-shiryen zagaye na uku na zuba ruwan dagwalon a teku bayan an kammala zagaye na biyu na zubar da dagwalon kuma an gudanar da ayyukan kiyayewa da tabbaci. (Yahaya)