logo

HAUSA

Masar ta gudanar da taro kan yadda za a kawo karshen tashe tashen hankula a Gaza

2023-10-22 17:00:33 CMG

A jiya Asabar ne aka kammala taron zaman lafiya na kasa da kasa a sabuwar hedkwatar gudanarwa ta Masar da ke gabashin birnin Alkahira, inda shugabannin kasashe da ministocin kasashe da dama suka bukaci da a kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza. 

Taron wanda aka yi wa lakabi da babban taron zaman lafiya na birnin Alkahira, an fara shi ne da safiyar Asabar din nan, wanda shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya kira don neman hanyar sassauta rikicin Gaza, da neman tsagaita bude wuta, da kuma neman cimma matsaya kan dadadden rikicin Isra'ila da Falasdinu ta hanyar "samar da kasashe biyu."

Sisi a jawabinsa na bude taron ya ce, Masar ta yi Allah wadai da "hare-haren fararen hula" tare da bayyana mamakinta kan yadda duniya ta mayar da martani kan tabarbarewar jin kai a Gaza, 

Shugaban na Masar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka tarwatsa Falasdinawa suke kaura zuwa yankunan Masar, yana mai tabbatar da cewa magance batun Falasdinawa ba tare da samun mafita ta gaskiya ba "Ba zai faru ba kuma Masar ba zata yarda da hakan ba."

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya jaddada cewa, za a iya samun zaman lafiya da tsaro ne kawai ta hanyar "samar da kasashe biyu" da warware matsalar 'yan gudun hijira bisa kudurin MDD mai lamba 194.

A nasa bangaren, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a daidaita batun Palasdinu ta hanyar "samar da kasashe biyu". Ya kuma yi maraba da shigar ayarin motocin kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar zuwa Gaza a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul-Gheit a nasa jawabin ya ce dole ne kasashen duniya su yi kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza da kuma kawo karshen hare-haren bam da Isra'ila ke kaiwa kan fararen hula a zirin Gaza.

Shi kuwa sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly, ya ce ra’ayin Birtaniyya a fili yake, kuma a ko da yaushe tana bayyana cewa Isra’ila na da ‘yancin kare kai da kuma ‘yancin ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba. (Yahaya)