logo

HAUSA

Masar da MDD sun tattauna kan yadda za ta kwantar da hankali tare da isar da agaji zuwa Gaza

2023-10-20 13:48:21 CMG Hausa

A jiya ne, ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry, ya tattauna da babban sakataren MDD Antonio Guterres, kan hanyoyin dakile rikicin Isra’ila da kungiyar Hamas, da shirye-shiryen isar da kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza da aka yiwa kawanya.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar bayan ganawarsu a birnin Alkahiran Masar, Shoukry ya ce ya tattauna da Guterres kan rikicin da ake fama da shi, wanda ya kara jaddada kiran da MDD ta yi na gaggauta tsagaita bude wuta.

Tattaunawar tasu ta zo ne kwana guda, bayan da Isra'ila ta amince ta bar wasu kayan agaji da Masar, da wasu kasashe da kungiyoyi ke bayarwa zuwa Gaza ta mashigar Rafah da ke tsakanin Masar da yankin Falasdinu, wanda Isra'ila ta katange baki daya, da kuma rashin samar da ababen more rayuwa da kai harin bama-bamai akai-akai.

Tashar talabijin ta Al-Qahera dake Masar ta ruwaito cewa, akwai manyan motoci makare da tarin kayan agaji da kasashe da dama da hukumar lafiya ta duniya WHO suka bayar a baya-bayan nan dake tsaye a bangaren Masar, suna jiran tsallakawa zuwa Gaza Jumma’ar nan.

Ministan ya bayyana cewa, shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya shirya gudanar da taron zaman lafiya a birnin Alkahira gobe Asabar, inda za a yi kokarin tsagaita bude wuta tare da jaddada muhimmancin kai agajin jin kai zuwa Gaza. (Ibrahim)