logo

HAUSA

A shirye kasar Sin take ta taka muhimmiyar rawa wajen saukaka tankiyar dake tsakanin Falasdinu da Isra’ila

2023-10-20 14:24:46 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin na musamman kan harkokin Gabas ta Tsakiya ya jaddada shirin kasar Sin na taka muhimmiyar rawar da ta kamata wajen saukaka tankiyar dake tsakanin Falasdinu da Isra’ila, tare da ingiza tattaunawar zaman lafiya.

Zhai Jun ya bayyana haka ne yayin ziyararsa a yankin Gabas ta tsakiya.

Jakadan ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na bakin ciki da yanayin matsalar jin kai da aka shiga a yankin, haka kuma tana Allah wadai da dukkan ayyukan dake haifar da illa ga fararen hula tare da adawa da keta dokokin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana cewa ainihin dalilin da ya haifar da yanayin da ake ciki shi ne, gazawa wajen kare halaltattun hakkokin Falasdinawa. (Fa’iza Mustapha)