logo

HAUSA

Koci Djordjevic ya bayyana kyakkyawan fata ga ci gaban kwallon kwando a kasar Sin

2023-10-20 15:49:40 CMG Hausa

Babban kocin kungiyar kwallon kwando ta kasar Sin Aleksandar Djordjevic, ya ce a nan gaba kungiyar da yake jagoranta za ta kai ga cimma nasara. Koci Djordjevic wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, bayan rashin nasarar da kungiyar ta samu a wasanni biyu da suka gabata a bana.

Bayan rashin nasara da kungiyar ta samu a gasar kasa da kasa ta FIBA, inda ta zo matsayi na 29 a Manila, tare da rasa damar shiga jerin kungiyoyin da za su fafata a gasar Olympic ta birnin Paris a shekarar 2024 dake tafe, kungiyar ta Sin ta kuma yi rashin nasara a gasar wasanni ta Asiya da aka kammala a Hangzhou, inda ta gaza kare kambin kwallon Kwando a gasar, bayan da kungiyar kasar Philippine ta yi galaba kan ta Sin a wasan kusa da na karshe.

Bayan wadannan abubuwa da suka faru, shugaban hukumar kwallon kwando ta Sin Yao Ming, ya dauki cikakken alhakin hakan, tare da amincewa da duk wani sakamako da zai biyo bayan hakan, kana ya ki amincewa ya yi tsokaci game da cikakken shirin sauya tsare-tsaren kungiyar, wanda ake hasashen zai kawo babban garanbawul ga kungiyar. Sai dai duk da haka, ya ce shawarwarin koci Djordjevic wanda dan asalin kasar Sabia ne za su taimaka.

Djordjevic mai shekaru 56 da haihuwa, wanda ya taba jan ragamar kungiyar kwallon kwando ta Sabia tsakanin shekarun 2013 zuwa 2019, ya karbi ragamar kungiyar Sin, yayin da ake tsaka da fama da annobar COVID-19, inda ya fara da zabar kwararrun ‘yan wasa Sinawa, tare da fara sabawa da salon wasan su yayin buga gasar CBA ta kasar Sin.

Daya daga shawarwarin da ya baiwa hukumar shirya wasan kwallon kwando ta Sin shi ne sauya lokacin buga wasa daga mintuna 48 zuwa 40 a gasannin cikin gida.

A cewar Djordjevic, "Wasannin da hukumar FIBA ke shiryawa masu kunshe da mintuna 40, sun saba da na mintuna 48. Wannan ce shawara da na ke so a lura da ita a tsarin buga wasannin kwallon kwando na kasar Sin. Dalili na a nan shi ne, muna son mu cimma nasara ne cikin mintuna 40 ba 48 ba".

Djordjevic ya hakaito kalaman babban kocin kwallon kwando na Amurka Steve Kerr, wanda ya bata cewa "Cikin mintuna 48, ‘yan wasa na iya yin kasa da maki 20, kana su farfado, amma a mintuna 40 wata kila a rasa irin wannan dama".

Kocin Djordjevic ya kara da cewa, "Yanayin wasa, da karfin wasa, da yanayin tunani, da dabi’un wasa da ‘yan wasa suka koya cikin shekara guda, ta hanyar buga wasa nau’i daya ba zai yiwu a sauya shi lokaci guda ba. Wani dan wasa ya taba zuwa gare ni, ya tambaye ni hutun dakika 20, bai san cewa ba bu wannan damar a tsarin gasar da hukumar FIBA ke shiryawa ba”.

 

A daya bangaren kuma, kocin ya yi tsokaci da cewa, akwai banbanci tsakanin yadda alkalan gasar kwallon kwando ta kasar Sin ko CBA suke gudanar da alkalanci, da yadda abun yake a ka’idojin gasar FIBA. Djordjevic ya ce ya kamata alkalan wasan na Sin su samu wani horo a Slovenia, ta yadda za su koyar da ‘yan wasa Sinawa ka’idojin wasan na hukumar FIBA.

Ya ce "Mun yi taro a baya, a lokacin na nuna musu bidiyon wasan da muka yi da Croatia, na yiwa ‘yan wasa na bayani game da yadda ‘yan wasan Croatia suka rika jan ra’ayin alkalin wasa. Na tambayi ‘yan wasa na game da ra’ayin su, cewa ko akwai laifi da suka gani an aikata? Kuma har ma a lokacin kyaftin din su Zhou Peng, ya ce idan da a gasar CBA ne alkalin wasa ba zai hura ba da laifi ba".

Djordjevic ya kara da cewa, akwai lokutan da ‘yan wasan kwallon kwando na Sin ke sabawa dokokin hukumar FIBA, kamar lokacin da dan wasan kasar Hu Jinqiu, ya karya irin wannan doka yayin wasan da suka buga da Serbia a gasar cin kofin duniya, wanda hakan a cewar koci Djordjevic, na da alaka da rashin kwararrun alkalan wasa da suke busa gasar CBA ta kasar Sin.

Bayan rasa gurbi a gasar Paris dake tafe, yanzu haka kungiyar Sin ta karkata ga shirin tunkarar gasar 2028 da za a buga a birnin Los Angeles na Amurka, za ta kuma yi duk abun da ya dace domin kaucewa rashin nasara. ‘Yan wasan kungiyar matasa ne masu karancin shekaru, wato masu matsakaitan shekaru 25, su ne kuma suka buga gasar Asiya da aka kammala, sabanin ‘yan wasan Philippine masu matsakaitan shekaru 32, sai dai kuma abu ne mai wahala, a kawar da kai game da yadda kasar Qatar ta shiga gasar da ‘yan wasa 2 masu shekaru kasa da 16, wato Mohamed Ndao da Abdulla Mousa. Abu ne a fili cewa, yana da wahala ‘yan wasan Sin Zhao Rui mai shekaru 27, da Zhao Jiwei mai shekaru 28 a yanzu, su iya kaiwa har shekara ta 2028, ana iya kuma cewa kungiyar ‘yan wasan kwallon kwando ta Sin ba ta da isassun ‘yan wasa masu karancin shekaru da za su iya maye gurbin na yanzu cikin sauri.

Game da hakan, koci Djordjevic na ganin ya dace hukumar CBA ta jingine wa’adin shekarun ‘yan wasa, wato daga 18 zuwa sama, ta amince da tattaro ‘yan wasa masu karancin shekaru da za su samu kwarewa nan gaba kadan. Ya ce ana iya tuna ‘yan wasa kamar Toni Kukoc, da Vlade Divac, wadanda a shekarun 1987 suka buga gasar FIBA ta ‘yan kasa da shekaru 19, dukkanin su sun fara buga wasa a ajin kwararru tun suna da shekaru 16.

Koci Djordjevic ya ce tun da CBA ta gabatar da taron manema labarai a makon jiya, abu ne mai yiwuwa a iya sauya wa’adin mafi karancin shekarun daukar ‘yan wasa, domin hakan zai taimakawa kungiyar kaiwa ga nasara a wasannin kasa da kasa.

Djordjevic ya kara da cewa "Me zai hana a shigo da tsarin gayyatar ‘yan wasan ketare don buga gasar cikin gida? Idan ba bu damar ‘yan wasa su rika sauya kungiyoyin su akai-akai kamar yadda ake yi a turai, to kamata ya yi Sin ta amince da shigowar ‘yan wasan ketare cikin gasannin cikin gida. Hakan zai bunkasa gasannin, da karfafa fahimtar dabarun wasa, tare da baiwa ‘yan wasan Sin karin damammaki na buga gasanni tare da ‘yan wasan kasashe daban daban.

Ya ce “Idan mun kalli gasar CBA, za mu ga cewa, dukkanin kungiyoyin na da ‘yan wasa da ba kasafai suke buga wasa ba, don haka ba batu ake yi na ‘yan wasan ketare su karbe damar wasa ta ‘yan wasa Sinawa ba”.

Sai dai a wata tattaunawa da ta gabata da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Yao ya bayyana cewa, kwangilar da aka kulla da Djordjevic za ta kare ne zuwa karshen shekarar nan. Kuma tabbas da yawa daga masu sha’awar kwallon kwando a kasar Sin, ba su gamsu da salon da mai horas da ‘yan wasan na kasar Serbia ke bi ba, suna ganin bai dace kocin ya bar dan wasan tsakiya Hu Jinqiu a benci ba, yayin wasan cin kofin duniya da kungiyar ta buga.

Sai dai a nasa bangaren, yayin da yake kare salon horas da ‘yan wasa da yake aiwatarwa, koci Djordjevic ya ce “A wasu lokuta mai horaswa kan nacewa wasu ra’ayoyi, wato ba ko da yaushe ne ake yin kuskure ba, kana ba ko da yaushe ake yin daidai ba. Abu ne mai sauki ka ji wani ya ce me yasa ba ka saka wane a wasa ba, shi ne zai iya warware matsala. Amma gaskiya ba haka abun yake ba, saboda komai na bukatar dogon lokaci na tsare tsare, buga wasa matakin karshe ne kawai na neman samun nasara". Duk da cewa ba bu tabbas, game da makomar sa a kungiyar Sin, koci Djordjevic ya tabbatar da cewa, zai ci gaba da aiki tukuru muddin yana tare da kungiyar ta kasar Sin. Ya ce "Har kullum kofa ta a bude take, game da batun horas da ‘yan wasan kasar Sin, idan har an bukaci tattaunawa da ni".