logo

HAUSA

Kamfanin jiragen sama na kasar Uganda ya kaddamar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye zuwa Najeriya

2023-10-20 10:08:19 CMG Hausa

Kamfanin jiragen sama na Uganda, mamallakin jirgin fasinja da jigilar kaya a gabashin Afirka, ya kaddamar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye daga filin jirgin sama na Entebbe zuwa Lagos, cibiyar tattalin arzikin Najeriya, a wani yunkuri na bunkasa alaka da kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar. 

Kamfanin ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar cewa, jirgi ya yi jigilar farko a ranar Alhamis biyo bayan samun amincewar hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama a Uganda da Najeriya. “kamfanin jiragen na Uganda zai rika zirga-zirga zuwa Najeriya sau uku a mako, a ranakun Litinin, Alhamis da Lahadi, ta hanyar amfani da babban jirginsa Airbus A330-800neo mai kujeru 258.

Jenifer Bamuturaki, babban jami’ar gudanarwa na kamfanin, ta ce an shirya jadawalin tashi da saukar jirgin ta yadda za a samar da hanyoyin da za a iya kaiwa ga sauran wuraren da ke da karancin lokacin jira. (Muhammed Yahaya)