logo

HAUSA

Harin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar farar hula a yankin arewa mai nisa na Kamaru

2023-10-20 13:51:04 CMG Hausa

Farar hula guda ya rasa ransa sanadiyyar wani harin kungiyar Boko Haram, ranar Laraba da dare a yankin arewa mai nisa na Kamaru.

Wata majiya da ta nemi kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya sakaya sunanta, ta bayyana cewa, harin da mayakan suka kai yankin Goldavi, ya yi sanadin mutuwar wani mai suna Dayagoue tare da batar wasu 3, tana mai cewa akwai yiwuwar mayakan ne suka sace su.

Kafofin watsa labarai na Kamaru sun ruwaito cewa, tun daga farkon bana, kungiyar Boko Haram ta kara matsa kaimi wajen kai wa fararen hula da sojoji hare-hare. (Fa’iza Mustapha)