logo

HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya tsawaita haramcin fitar da mai daga kasar Libya

2023-10-20 11:02:04 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri na tsawaita dokar hana fitar da man fetur daga kasar Libya ba bisa ka'ida ba.

Kuduri mai lamba 2701, wanda ya samu goyon bayan bai daya na mambobin kwamiti din su 15, ya tsawaita dokar na tsawon watanni 15, har zuwa ranar 1 ga Fabrairu, 2025.

Ya bukaci dukkanin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su bi tsarin takunkumin da aka kakkabawa kasar Libya, wadanda suka hada da takunkumin makamai, hana zirga-zirga, da hana kadarori, tare da yin kira ga dukkan kasashe mambobin da kada su tsoma baki a rikicin kasar Libya, ko kuma su dauki matakan da za su kara ta'azzara rikicin.

Kwamitin ya bukaci dukkan bangarorin dake Libya da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta ranar 23 ga Oktoba, 2020, tare da yin kira ga kasashe mambobin kungiyar da su mutunta da goyon bayan cikakken aiwatar da yarjejeniyar, gami da janyewar dukkan sojojin kasashen waje da sojojin haya daga Libya ba tare da jinkiri ba. (Muhammed Yahaya)