logo

HAUSA

Sin ta yi matukar takaici da matakin da Amurka ta dauka na dakatar da kudurin jin kai a Gaza

2023-10-20 13:37:34 CMG Hausa

Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana yayin ganawa da manema labarai na yau da kullum jiya Alhamis cewa, kasar Sin ta yi matukar takaicin yadda Amurka ta ki amincewa da kudurin kwamitin sulhu na MDD, wanda ya kai ga a dakatar da ayyukan jin kai a Gaza.

A ranar Laraba ne dai, kudurin da Brazil ta gabatar, ya samu goyon bayan kasashen kwamitin 12 daga cikin 15. Amurka, wacce ke da ikon hawa kujerar naki, ita ce mamba daya tilo da ta kada kuri'ar kin amincewa da kudurin, yayin da kasashen Birtaniya da Rasha suka kauracewa kada kuri’a.

Mao ta bukaci kwamitin sulhun da ya saurari kiran da kasashen Larabawa da al'ummar Palasdinu suka yi, da taka rawar da ta dace wajen ganin an tsagaita bude wuta, da kare fararen hula da kuma hana fadadar bala'in jin kai.(Ibrahim)