logo

HAUSA

Yadda ake fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a zirin Gaza

2023-10-19 10:22:49 CMG

Hotunan yadda ake fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a zirin Gaza. Isra’ila na samar da kimanin kaso 2/3 na wutar lantarki da ake amfani da shi a zirin Gaza. A ranar 7 ga wata, ma’aikatar makamashi ta Isra’ila ta sanar da katse wutar lantarki da ake samarwa ga zirin Gaza, a matsayin martani ga rikicin da ya barke tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila. MDD ta kuma yi gargadin cewa, matsalar jin kai da ake fuskanta a zirin Gaza na kara tabarbarewa, inda ya yiwu makamashi da abinci da ruwa za su kare cikin dan kankanin lokaci.