Shugabannin Masar da Amurka sun amince da samar da taimako ga zirin Gaza ta mashigar Rafah
2023-10-19 11:37:46 CMG Hausa
Fadar shugaban kasar Masar ya bayar da sanarwa a safiyar yau 19 ga wata cewa, shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi ya kira shugaban kasar Amurka Joseph Biden ta wayar tarho a ranar 18 ga wata, inda suka amince da samar da taimako mai dorewa ga zirin Gaza ta mashigar Rafah. Bisa sanya ido da MDD za ta yi musu, hukumomin kasashen biyu da abin ya shafa za su hada kai da kungiyoyin jin kai na duniya don tabbatar da isar kayayyakin tallafi zirin yadda ya kamata.
A ranar 18 ga wata, ofishin firaministan Isra’ila ya bayar da sanarwar cewa, majalisar ministocin kasar ta amince da cewa, Isra’ila ba za ta hana kayayyakin ceto na jin kai shiga cikin zirin Gaza ta iyakar Masar ba, amma za su hana kungiyar Hamas samu kayayyakin. Kana idan Hamas ba ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su ba, to ba za a amince da kayayyakin ceto su shiga zirin Gaza ta iyakar Isra’ila ba. (Kande Gao)