Yadda kasar Sin ke ba da gudummawar zamanintar da kasashen duniya cikin shekaru 10 masu zuwa
2023-10-19 11:33:33 CMG
Zamanintar da kasashen duniya buri na bai daya ne da al’ummar duniya ke neman cimmawa, sai dai kuma aiki ne mai wahala da suke fuskanta. Kawo yanzu, kasashe sama da 20 ne a duniya suka kasance na zamani. Ta yaya kuma kasashe masu tasowa za su cimma burinsu na zamanintar da kansu? A gun bikin kaddamar da taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” (BRI) karo na uku a jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin cewa, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da kasa da kasa bisa shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, don ba da gudummawar zamanintar da kasa da kasa. A gun bikin, shugaba Xi Jinping ya kuma sanar da wasu matakai takwas na tallafawa aiwatar da shawarar cikin inganci.
A baya, kasashe masu tasowa da yawa sun rungumi salon kasashen yamma a matsayin hanya daya kacal da za a bi wajen zamanintar da kai, sai dai salon na kasashen yamma ba su dace da asalin yanayin kasashen da ke tasowa ba, don haka ma suke fatan gano sabuwar hanyar da za su bi. A cikin shekaru 10 da suka wuce, shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta tabbatar da cin moriyar juna a tsakanin kasar Sin da kasashen da abin ya shafa, wadda kuma ta samar da mafita ga kasa da kasa wajen zamanintar da kansu cikin shekaru 10 masu zuwa. (Lubabatu)