logo

HAUSA

Shugabannin kasashe da dama sun bayyana niyyarsu ta hada hannu wajen aiwatar da shawarar BRI

2023-10-19 10:28:50 CMG

Shugabannin kasashe da kungiyoyin duniya da dama sun bayyana cewa, shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” (BRI) ta sa kaimi ga bunkasuwar kasa da kasa, don haka suke son zurfafa hadin gwiwa, don aiwatar da shawarar cikin karin inganci.

Shugabannin sun yi kalaman ne yayin da suka halarci bikin kaddamar da taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” karo na uku a jiya Laraba a birnin Beijing.

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya yi nuni da cewa, yadda kasashen Afirka da Sin suke aiwatar da shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” ya sa kaimi ga raya cinikayya a tsakanin kasashen Afirka da ma cinikayya a tsakanin kasashen da kasar Sin, matakin da ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka.