logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya kaddamar da kamfanin harhada motoci na Sin a birnin Kpone

2023-10-18 20:30:03 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kaddamar da kamfanin harhada motoci na kasar Sin a birnin Kpone, dake babban yankin Accra.

Kamfanin na Zonda Sinotruk, na da jarin da ya kai dala miliyan 30, an kuma kafa shi ne bisa hadin gwiwar yarjejeniya tsakanin ma’aikatar cinikayya da raya masana’antu ta Ghana, da kamfanin dillancin manyan motoci na Zonda, da kuma kamfanin kera motoci na Sinotruk.

Karkashin tsarin da aka tanada, kamfanin zai rika harhada manyan motocin gudanar da ayyuka a kasar ta Ghana.  (Saminu Alhassan)