Kasashe Masu Tasowa Da Abokai Sun Goyi Bayan Matsayin Kasar Sin Mai Adalci A Taron MDD
2023-10-18 11:00:41 CMG Hausa
A jiya ne, kasashe masu tasowa da abokai suka bayyana goyon bayansu ga kasar Sin a yayin babban taron muhawara kan batutuwan kiyaye hakkin dan Adam da kwamiti na uku na babban taron MDD karo na 78 ya shirya.
A jawabin da ya gabatar a yayin taron, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi karin haske kan ma'anar kare hakkin bil Adama a cikin shawarar tabbatar da tsaro a duniya, da shawarar raya kasa da kasa, da ta wayewar kai a duniya, inda ya gabatar da matakan kare hakkin dan Adam mai halayyar kasar Sin, da muhimman nasarorin da Sin ta cimma, inda ya nuna adawa da karyar da kasashen yammaci ke kirkira game da yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin
A bayanan da suka gabatar, kasashe da dama sun yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen kare hakkin dan Adam. An dunkule wadannan kalamai zuwa wata babbar murya mai nuna goyon baya da bayyana matsayin kasar Sin na adalci, da adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam.
A madadin kasashe 72, kasar Pakistan ta gabatar da sanarwar hadin gwiwa, don nuna goyon baya ga adalcin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Xinjiang da Hong Kong, da kuma Xizang.
Ita ma kasar Venezuela, a madadin kasashe 19 mambobin rukunin abokai dake kare kundin tsarin MDD, sun ba da sanarwar hadin gwiwa, don nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin, tare da yin watsi da ma sukar ayyukan da Amurka da wasu makiya na kasashen yammacin duniya ke yi, kamar nuna fuska biyu a fannin kare hakkin dan Adam, da hada baki wajen nuna wariyar launin fata, da cin zarafi ta hanyar tilastawa na kashin kai, da tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu kasashe.(Ibrahim)