logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Duniya Da Su Taimaka Wajen Samar Da Zaman Lafiya A Yankin Manyan Tabkuna Na Afrika

2023-10-18 11:14:06 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Manyan Tabkuna na Afrika.

Dai Bing ya yi kiran ne a jiya, yayin bude taron kwamitin sulhu na MDD kan yankin Manyan Tabkuna na Afrika.

A cewarsa, batun tsaro a yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, shi ne babban kalubale a yankin. Ya ce kasashen yankin sun dogara da juna a fannin tsaro. Kuma a halin da ake ciki, akwai bukatar kasashen su yi amfani da tsare-tsaren zaman lafiya na Nairobi da Luanda, su hada hannu wajen kiran kungiyoyi masu dauke da makamai su dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da kuma saukaka yanayin dar-dar da ake ciki ta hanyar tattaunawa.

Dai Bing ya ce, yayin da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na 3 ke gudana a Beijing, kasar Sin na sa ran hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da kasashen dake Manyan Tabkuna, wajen raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya mai inganci, da aiki tare wajen samun ci gaba na bai daya da wadata da bayar da gudummuwa ga zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a yankin. (Fa’iza Mustapha)